Ephesians 2

An Rayar Tare da Kiristi

1A dā, ku matattu ne saboda laifofinku da kuma zunubanku. 2Kun yi rayuwa kamar yadda sauran mutanen duniya suke yi, cike da zunubi, kuna biyayya da Shaiɗan, wannan mai mulkin sararin sama. Shi ne ruhun nan da yanzu yake aiki a cikin masu ƙi biyayya ga Allah. 3Dukanmu mun yi irin rayuwan nan a dā, muna bin kwaɗayi da shaʼawace shaʼawacen jikunanmu da tunaninmu. Mun ba wa Allah haushi, kuma dā za a hukunta mu kamar sauran mutane. 4Amma saboda yawan ƙaunar da yake yi mana, Allah, wanda yake mai yawan jinƙai, 5ya ba mu rai saʼad da ya tashe Kiristi daga matattu. Ta wurin alherin Allah ne aka cece ku. 6Allah ya tashe mu tare da Kiristi ya kuma ba mu wurin zama tare da shi a cikin mulkin samaniya. 7Allah ya yi haka domin a zamanai masu zuwa yǎ yi amfani da mu a matsayin yalwar alherinsa da ya wuce misali, yadda yake a dukan abin da ya yi mana ta wurin Kiristi Yesu. 8Allah ya cece ku ta wurin alheri saʼad da kuka ba da gaskiya. Wannan kuwa ba yin ku ba ne, kyauta ce daga Allah. 9Ceto ba lada ba ne saboda abubuwa masu kyau da muka yi, don kada wani yǎ yi taƙama. 10Allah ya shirya mana mu yi abubuwa masu kyau mu kuma yi rayuwa kamar yadda kullum yake so mu yi. Shi ya sa ya aiko da Kiristi yǎ sa mu zama abin da muke.

Ɗaya Cikin Kiristi

11Kada ku manta cewa dā ku Alʼummai ne. A gaskiya ma, a dā masu kira kansu “masu kaciya,” suna ce da ku “marasa kaciya” (ga shi kuwa, kaciyar nan ta jiki ce, wadda ake yi da hannun mutum). 12A lokacin ba ku san Kiristi ba. A ware kuke daga mutanen Israʼila, kuma ba ku da dangantaka da alkawaran da Allah ya yi da su. Kun yi zama a duniyan nan babu bege kuma babu Allah. 13Amma yanzu a cikin Kiristi Yesu, ku da dā kuke can da nesa an kawo ku kusa ta wurin jinin Kiristi. 14Gama shi da kansa ne ya kawo salama a tsakanin Yahudawa da Alʼummai wanda ya mai da biyu nan suka zama ɗaya, ya rushe katangan nan ta ƙiyayya wadda ta raba mu. 15Kiristi ya ba da jikinsa don yǎ kawar da doka da dukan umarnanta da ƙaʼidodinta. Ya yi haka domin yǎ halicci sabuwar zuriya daga zuriyan nan biyu. Ta haka kuma yǎ kawo salama tsakaninsu. 16A kan gicciye Kiristi ya kawar da ƙiyayyar da take tsakaninmu da juna. Ya kuma kawo salama tsakaninmu da Allah. 17Ya zo ya yi muku waʼazin salama; ku da kuke nesa da shi, ya kuma yi wa waɗanda suke kusa. 18Gama ta wurinsa dukanmu za mu iya zuwa gun Uba ta wurin Ruhu guda.

19Don haka, yanzu ku ba baƙi ba ne, ku kuma ba bare ba ne. Ku ʼyan ƙasa ne tare da mutanen Allah, iyalin gidan Allah kuma. 20Ku gini ne wanda manzanni da annabawa suke tushensa, Kiristi kuma shi ne dutse mafi muhimmanci. 21Shi ne yake riƙe dukan ginin a haɗe yake kuma sa yǎ yi girma yǎ zama haikali mai tsarki domin Ubangiji. 22Ku ma sashe ne na wannan ginin da Kiristi ya yi inda Allah yake zaune ta wurin Ruhunsa.

Copyright information for HauSRK